Buhari ya kaddamar da Aikin Hanyar Janguza zuwa Dayi a Kano

Date:

Daga Musa Abdullahi Kano

Gwamnatin tarayya zata Kashe Sama da Naira Biliyan 62 wajen Gina Hanyar data tashi Daga Janguza zamu kabo , Gwarzo har zuwa Dayi dake jihar Katsina .

Ministan Ma’aikatar aiyuka da Gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan Yayin kaddamar da Aikin Hanyar wadda a Garin Dansudu dake Karamar Hukumar Tofa ta jihar Kano.

Ministan Wanda Daraktan Manyan Hanyoyi na gwamnatin Tarayya Engr. Essen yace gwamnatin ta bayar da Aikin Hanyar ne Saboda irin muhimmancin da yake dashi ga Al’ummar jihohin Kano da Katsaina.

Yace tsayin Hanyar ya Kai Kilomita 82 , Kuma za’a kammala Aikin ne a Nan da Shekaru buyu Masu zuwa.

A Jawabinsa Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje yace Aikin Hanyar Zai taimaka wajen rage hadduran da ake samu a hanyar,tare kuma da bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya yabawa Shugaban kasa Muhd Buhari bisa irin aikyukan da ya yiwa al’ummar jihar Kano Kuma yace Aiyukan Suna Kara Daga darajar jihar Kano kasancewarta Cibiyar kasuwanci.

Yace Gwamna jihar Kano zata biya Diyya ga duk Masu kaddarorin da Suka chanchanci biyan Diyya a hanyar.

Sanata Kano ta Arewa Barau I Jibril shi ne ya gabatar da Kudirin Aikin a gaban Majalisar Dattawa har ya tabbata ya bukaci Yan kwangilar da zasu gudanar da Aikin Hanyar dasu Mai da hankali wajen kammala Aikin akan lokacin da aka debar musu.

Sanata Barau bayan ya yabawa Shugaban kasa Muhd Buhari ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa Gudunmawar daya bayar wajen tabbatuwar Aikin Hanyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Yusuf ya taya Dangambo murnar zama shugaban kungiyar mawallafa labarai ta internet na Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Hajjin bana: Za mu yi duk abun da ya dace don kyautata walwalar alhazan Jihar Kebbi – Amirul Hajji

Daga Ibrahim Sidi Muhammad Jega.   Shugaban kwamitin aikin hajin bana...

Bayan dawo da Gwadabe Anti daba, Yansanda sun kama yan daba 33 a Kano

Daga Rahama Umar Kwaru   Rundunar Yansanda ta Kasa reshen jihar...

Sabon Rikici ya Barke a Jam’iyyar NNPP ta Karamar Hukumar Dawakin Tofa

Rikici ya barke a cikin jam’iyyar NNPP ta karamar...