Kano Pillars ta hau matsayi na daya bayan ta doke Enyimba

Date:

Zaharadeen saleh

Kungiyar kwallon kafa ta kano pillars ta hau matsayi na daya bayan data samu nasarar doke kungiyar Enyimba International daci biyu da daya, a cigaba da gasar cin kofin kwallon kafa ajin firimiya ta nigeria, a zagayen wasa mako na 25 da aka shiga a lahadin nan a kakar wasa ta 2020/2021.

Tunda farko dan wasa Enyimba ne mai suna Victor mboama ne ya jefa kwallo aragar kano pillars a mintina bakwai da fara wasan.

An kai kimani mintina 56 dan wasan kano pillars mai suna Rabi’u Ali ya rama kwallon ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaran gida, a mintina 75 dan wasan kano pillars Ifeanyi ya kara kwallo ta biyu.

Yanzu haka bisa wannan nasara da kano pillars ta dawo matsayi na daya da maki 48, sai kungiyar Akwa united fc tana matsayi na biyu da maki 46 bayan data buga biyu da biyu da wikki Tourits a jihar bauchi.

Ga sakamakon ragowar wasanin da aka buga na mako na 25

Enugu Rangers 1 v MFM fc1
Kwara utd fc 3 v Jigawa G. Stars 0

Adamawa utd 0 v Plateau utd 2

Abia warriors 1 v fc Ifeanyi ubah 1

Dakkada fc 0 v Lobi stars 1

Heartland fc 2 v Rivers utd 2

Warri wolves 2 v sunshine 1

Katsina utd 2 v Nasarawa utd 1

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...