Daga Ibrahim Sani
Gwamnatin tarayya ta Bukaci Dukkanin Kafafen yada labaran Radio da Talabijin a Kasar Nan dasu Rufe Shafinkansu na Twitter.
Hukumar kula da Kafafen yada labaran Radio da Talabijin ta Kasa ce ta bayyana hakan Cikin Wata sanarwa da Mai dauke da sa hannun Daraktan yada labaran Hukumar Farfesa Amstrong Idanchaba.
Sanarwar Hukumar tace ya Zama wajibi Kafafen yada labaran subi Umarnin da Gwamnatin tarayya ta Dauka na Dakar da Twitter a Nigeria.
NBC tace Rashin kishi ne Kafafen yada labaran Kasar nan su cigaba da amfani da dakatacciyar kafar ta Twitter wajen yada labarai ko Daukar labaran.
Tace Akwai dokokin Hukumar da suka baiwa Hukumar damar tabbatar da Wannan Mataki na gwamnatin Tarayya.
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya Kamfanin Twitter ya goge wani Rubutu da Shugaban Kasa Buhari yayi akan Tsagerun kudu Maso gabas Masu rajin kada Kasar Biafra.