Sojojin Najeriya sun ‘kashe’ ‘yan ISWAP guda 50

Date:

Mayaƙan ƙungiyar ISWAP fiye da 50 ne rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe a Jihar Borno ranar Laraba.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Yerima Mohammed, ya ce dakarunsu sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar ne yayin da suka yi yunƙurin kai hari a Ƙaramar Hukumar Damboa da ke Borno.

Dakarun rundunar musamman ta Operation Hadin Kai ne suka samu nasarorin tare da taimakon sojojin sama, a cewarsa.

“‘Yan ta’addan sun kai hari garin da dukkan ƙarfinsu da manyan motoci masu ɗauke da bindigogi guda 12 da makaman harbo jirgi da babura da kuma ababen fashewa,” a cewarsa cikin wata sanarwa.

“Jajirtattun sojojin sun daƙile harin sannan suka lalata motoci masu silke tare da kashe ‘yan ta’addan ISWAP 50, abin da ya sa wasu suka tsere sakamakon luguden wuta daga sojojin sama.”

Da yake mayar da martani kan lamarin, Babban Hafsan Sojan Ƙasa Manjo Janar Faruk Yahaya ya taya dakarun murna game da nasarar da suka samu.

A wannan makon ne ƙungiyar ta sanar da naɗa Albarnawiy a matsayin shugabanta bayan ta yi iƙirarin kashe shugaban Boko Haram Abubakar Shekau.

98 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...