Zaharadeen saleh
Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba international dake garin aba, jihar abia ta fita daga gasar cin kofin kwallon kafa ta zakarun kungiyoyin nahiyar afrika ta caf confederation cup, a zagayen wasa na dab dana kusa dana karshe.
Kungiyar Enyimba fc ta fita daga gasar ne bayan data buga daya da daya da kungiyar Pyramid fc ta kasar masar a zagayen wasa na biyu da suka fafata a garin aba, bayan da a zagayen farko tayi rashin nasara daci hudu da daya a birnin cairo.
A yanzu kungiyar enyimba fc ta fita daga gasar confederation cup din ne da adadin kwallo biyar da biyu.
Kungiyar Enyimba fc itace kungiya daya tilo data rage a tsakanin kungiyoyi guda hudu suke wakiltar Nigeria a gasar zakarun nahiyar afrika.
Idan za’a iya tunawa tun a zagayen farko aka fitar da kungiyar kano pillars da plateau united ita kuwa kungiyar Rivers united a zagaye na kungiyoyi 32 aka fitar da ita.