Fadan Daba: Yan Sanda sun Kama Matasa 30 a Kano Yayin Bikin Sallah

Date:

Daga Nafi’u Lawan Dan Salo


Yayin da aka kammala shagulgulan Bikin Sallah Karama Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen jihar Kano tayi holin Wasu Matasa Kimanin su 30 wadanda aka Kamo a wurare daban-daban bisa zarginsu da yin fadan Daba lokacin bukukuwan Sallah Karama.


Kadaura24 ta rawaito Mai Magana da yawun Rundunar Yan Sanda ta Kano DSP Abdullahi Haruna kiyawa ne ya bayyana hakan Cikin Wani faifen video Daya wallafa a Sahihin shafinsa na Facebook.


DSP Kiyawa yace Yan Sanda anti-Daba ne suka kamo matasan wadanda aka nuna hotunan su kowannensu Yana time da makamin da aka kamasu dasu a Yayin da suke tsaka da farma junansu.


Wasu daga Cikin Matasa da DSP Kiyawa ya zanta dasu sun tabbatar da cewa an kamo su ne Yayin da suke fadan Daba a yankunansu.


Kadaura24 ta rawaito Kakakin Rundunar Yan Sanda yace Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano CP Sama’il Shu’aibu Dikko ya bada Umarnin dauke Matasan Daga ofishin anti Daba dake tal’udu zuwa Babban Sashin bincike na Rundunar dake Bompai domin gudanar da bincike tare da tura su kotu don girbar abin da suka shuka

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...