Daga Surayya Abdullah Tukuntawa
Gwamnatin Tarayya tace ba ta gaggawa don kara farashin man fetur ba, a cewar Timipre Sylva, Karamin Ministan Man Fetur
Sylva ya bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga shawarar kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) cewa tana bukatar farashin mai ya koma N380 ko N408.5 ga kowane litre.
A wani taro da suka gabatar, gwamnonin sun nemi a yi wa dokar kwastam ta kasa kwaskwarima tare da cire tallafin mai ba tare da bata lokaci ba, suna masu cewa tsarin tallafin da ake bayarwa a yanzu ba mai dorewa ba ne, kuma masu fasa-kwauri da ‘yan kasuwa da ke cinikin ta haramtacciyar hanya ne kawai ke cin gajiyar sa.
Shawarwarin da gwamnonin suka bayar sun haifar da fushi da fusata al’ummar a duk fadin kasar nan kamar yadda yawancin ‘yan Najeriya suka ce zai kara wahala a kasar.
Amma a nasa martanin, Sylva ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa ba za a kara farashin mai a watan Yuni ba.
“Ya zama dole a tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa duk da irin dimbin nauyin da ke tattare da tattalin arziki, Gwamnatin Tarayya ba t gaggawa take ba don ta kara farashin Man fetur don yin la’akari da gaskiyar kasuwar yanzu.”
“Dangane da wannan, Ina so in yi kira ga masu sayar da kayayyakin man fetur da su guji shiga duk wasu ayyuka da ka iya kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki da rarraba su a yayin da nake kira ga jama’a da su guji karbar irin wancan rahoton saboda Kamfanin Man Fetur na Najeriya ( NNPC) yana da wadataccen man fetur don sayarwa al’ummar kasar nan Cikin Sauki