Sallah: Tallafawa Marayu da Nakasassu 500 da Gidauniyar BUA tayi a Kano ya nuna tsantsar kishin Kano- Dr Zahra’u Umar

Date:

Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa

Kwamishiniyar harkokin Mata da walwalar al’umma ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhd Umar ta yabawa Gidauniyar BUA bisa bada tallafin kayan Abinchi da suturu ga Marayu da nakasassu 500 a jihar nan domin su gudanar da Bikin sallah Cikin Farin Ciki.

Dr Zahra’u Muhd Umar ta bayyana hakan ne yayin raba kayan agaji da Gidauniyar BUA FOUNDATION ta bayar a karkashin jagorancin Alhaji Abdussamad Ishaq Rabi’u wanda aka gudanar a makarantar koyon harshen larabci ta (S. A S) dake nan Kano.

Cikin Wata sanarwa da Jami’ar Hulda da jama’a ta Ma’aikatar Bahijja Malam Kabara ta Sanyawa hannu tace Kwamishiniyar ta kara da cewa, gudummawar ta zo a lokacin da ya dace, saboda za a yi bikin Karamar sallah Kuma hakan Zai fada wadanda suka amfana da tallafin suyi sallah Ciki Farin Ciki.

Ta kuma yi godiya ga Gidauniyar BUA FOUNDATION kan irin taimakon da suke yi wa talakawa da gajiyayyu, da kuma jan hankalin ga Sauran mawadata dake Cikin al’umma da suyi koyi da Wannan Gidauniyar don samun kyakkyawa lada a duniya da lahira.

Sarkin kutare da Sarkin Makafin jihar Kano sun nuna farin cikinsu ga wannan karamci da aka nuna musu a Wannan wata na Ramadan Mai Albarka.

A jawabinsu, mahaifan marayu da nakasassu sun nuna matukar jin dadinsu game da Wannan kabakin arziki da aka yi musu.

Wasu daga cikin Kayan da aka raba sun hadar da Kayan abinci, Tufafi Sai kuma Naira 500 ga kowane mutum.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...