Sallah: Shugaba Buhari ya bukaci a takaita bukukun Sallah Saboda Corona

Date:

Daga Aisha Uwais

 Yayin da Musulmai a Najeriya suka bi sahun sauran Musulmi a duniya wajen  shirye-shiryen bikin Karamar sallah  Shugaba Muhd Buhari ya bada umarnin  takaita dukkan bukukun saboda Annobar Coronavirus data addabi duniya.


 A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu Shugaban Kasar da Iyalansa da hadimansa, mambobin majalisar zartarwa da shugabannin hafsoshin tsaro wadanda suka zabi zama a Abuja za su hallarci sallah idi da karfe 09:00 na safe a fadar Shugaban kasa cikin bin ka’idojin kare Kai daga cutar COVID-19.


 Bayan haka Kuma Shugaban Kasar ba Zai karbi Masu zuwa Yi Masa Barka da sallah ba kamar yadda aka saba ,Inda ya umarci limamai Yan siyasa da Shugabanin gargajiya dasu gudanar da bukukun sallar a gidajen su don gudun yaduwar Annobar Coronavirus.


 Sanarwar ta nuna cewa Shugaba Buhari yana mika godiya ta musamman ga Ulama (Malaman Addinin Musulunci) da duk sauran shugabannin addini (Musulmi) wadanda ke ci gaba da yi wa kasar nan addu’o’in samun Zaman lafiya Mai dorewa.


 Shugaban, baya ga wannan, yana amfani da wannan dama don jajantawa duk wadanda suka rasa Yan uwansu Sakamakon Matsalolin tsaro dake faruwa a sassan kasar.


 Shugaban yana kira ga dukkan shugabanni da su ja kunnen matasan su tare da gargadin su kan amfani da su wajen tayar da fitina.

80 COMMENTS

  1. Усик Джошуа бій 25 вересня в Лондоні – все про поєдинок Энтони Джошуа Александр Усик Бой Усик – Джошуа пройдет 25 сентября в Лондоне. На кону в этом поединке будут стоять титулы чемпиона мира в супертяжелом весе по версиям ibf, wbo, wba и ibo, которыми владеет Джошуа.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta dakatar da nuna tallan maganin Gargajiya a Fina-finai da yawo a tituna

A wani mataki na tabbatar da bin ka'idoji tare...

Da dumi-dumi: NNPP ta nemi afuwar Tinubu kan kalaman suka da ake zargin Kwankwaso ya yi masa

  Jam’iyyar NNPP ta nemi afuwar Shugaban kasa Bola Tinubu...

Gwamnatin Kano ta dakatar da Dadin kowa, Labarina, Jamilun jidda da wasu fina-finai 19

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   A kokarinta na tabbatar da ana...

2027: Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana Matsayarsa kan takarar gwamnan Kano

Daga Zakariya Adam Jigirya   Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan...