Tahajjud: Yan Bindiga sun Sace Masallata 40 a Wani Masallaci dake Katsina

Date:

Akalla wasu bayin Allah Musulmi 40 ne ‘yan bindiga suka sace a yayin da suke gudanar da Sallah Tahajjud, wata sallar tsakar dare da ake gudanarwa a cikin watan Ramadan, a wani masallaci da ke garin Jibiya na jihar Katsina.


 Mazauna garin sun ce ‘yan bindiga da dama sun kai hari a masallacin da misalin karfe 2 na daren Litinin kuma suka tafi da masu ibadar.


 Rahotannin sun nuna cewa masu garkuwan da farko sun Debi masallata 47, ciki harda mata da yara, amma daga baya bakwai suka dawo.
 “Ya zuwa yanzu mun tabbatar mutane 40 ne suka bata yayin harin,” in ji wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunansa.


 Wani mazaunin garin Mai Suna Lawal Jibiya, ya ce mazauna kauyukan da suke kusa dasu sun sanar da su game da harin, bayan sun ga hucewar ‘yan bindigar da ke kan hanyar zuwa garin.


 Ya ce daruruwan matasa da ‘yan banga da ke cikin garin sun Yi shirin ko ta kwana don tunkarar’ yan ta’addan, amma maharan sai suka sauya hanyarsu ta shiga Garin suka shiga garin ta mashigar yamma.


 “Mun tsammacesu daga mashigar gabas ta hanyar Daddara, Kukar Babangida ko Magama amma sai suka wuce bayan gari suka yada zango a Jibawa.


 “Daga Jibawa daga nan suka zagaya zuwa mashigar yamma kusa da asibitin Yunusa Dantauri kuma suka farma wani masallaci a bayan gari,” in ji shaidar.


 A cewarsa, ‘yan fashin ba su yi harbi ba  har sai da suka gama aikin .


 Jibiya, wani gari ne da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Nijar, na daya daga cikin wuraren da ake yawan yin garkuwa da Mutane da kuma ayyukan ‘yan fashi.

89 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Dangote ya rage farashin man fetur a Nigeria

Matatar mai ta dangote ta rage farashin man fetur...

Muna bukatar kayan aiki domin magance matsalar tsaro a karamar hukumar Nasarawa – Muhd Haruna Black

Kwamandan Jami'an sintiri na karamar hukumar Nasarawa a jihar...

Da dumi-dumi: An Sanya dokar Hana fita a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon...

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...