Daga Usman Kofar Mata
Kungiyar masu sana’ar sayar da kayan Marmari ta kasa reshen jihar Kano ta danganta tsadar da farashin Kankana tayi a wannan shekara da matsalar tsaro da jihohin da ake noman kankanar ke fuskanta.
Bayanin hakan ya fitone ta bakin jamiin hulda da jamaa na Babbar Kasuwar sayar da kayan marmari dake Naibawa Malam Murtala Yunusa yayin wata ganawa da wakilin Kadaura24 a wannan mako.
Murtala Yunus yace “tabbas a bana an samu karancin kankana a wannan babbar kasuwar ta sayar da kayan marmari ta Naibawa, Dalilin tsadar kankanar kuwa shi ne gaskiya abana kusan jihohin da sukafi yin nomanta a nan Arewa abana ba suyi nomanta sosai ba saboda barazanar tsaro da suke fuskanta, kamar jihar Zamfara da jihar Niger da garin Geidam da Damaturu da kuma wani bangare na jihar Sokoto”. Inji Malam Murtala
” A gaskiya wadannan jihohi sune sukafi yin noman Kankana kuma sune suke cika wannan kasuwa da ita, amma abana saboda waccan dalili dana zayyana shine yasa basu yi nomanta ba kuma shine dalilin da yasa tayi karanci a kasuwar tunda babu ita” Inji Murtala Ayuba
“Sai dai ayanzu da muke wannan magana farashin Kankanar ya fadi kasa wanwar saboda yunkurin da karamar hukumar Bunkure ta nan jihar Kano tayi da kuma wasu kananan hukumomin jihar Jigawa na noma kankanar sosai tare da kawo ta wannan kasuwa, inda kamar yanda kake gani a yanzu kusan itace tafi kowanne kaya yawa a wannan kasuwa sabanin farkon kamawar watan Azumi da tayi matsanancin karanci a wannan Kasuwa” Inji Murtala.
Murtala ya kara da cewa abana musamman a farkon kamawar wannan wata na Azumin Ramadan farashin kankanar yayi tashin gwauran zabi inda ake saida buhunta mai daukar kankana guda dari a ciki akan naira dubu dari da doriya (100,000)amma kuma a yanzu baya wuce naira dubu hamsin (50,000) a tsayayyan farashin kasuwa.
Ya lasafta farashin Abarba da Gwanda da Ayaba a matsayin kayayyakin da sukafi Kankana tsada a bana, amma acewarsa hankakin mutane yafi daukuwa akan tsadar Kankana saboda itace mafi bukatuwa ga mai Azumi kamar yanayi ke nunawa.
Kazalika ya bukaci manya da kananan yan kasuwa masu sarin kayayyaki a Kasuwar dasu sassauta farashin Kankanar kamar yadda farashin ta ya sauka a kasuwar da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.