December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Wanene Badamasi Burji?


Daga Yakubu Garba Uba 

 Wanene Badamasi Burji?
 Alh.  An haifi Badamasi Buruji ne a ranar 15 ga Nuwamba, 1968, a ƙauyen Burji, shi mawallafi ne, ɗan kasuwa, marubuci, ɗan jarida kuma mai son taimakon jama’a, ya halarci makarantar firamare ta Burji central daga 1973 zuwa 1980 kafin ya tafi Kwalejin Fasaha ta Gwamnati, Wudil daga 1980 zuwa 1980  1985.
 Ya yi aiki tare da sashen kula da gandun daji a Birniwa, Wanda  yanzu haka ya ke Jihar Jigawa, bayan ya yi aiki a sashin gandun daji, daga karshe ya koma babban birnin Kano inda ya hade da kawunsa, Alhaji Salisu Hamza Kadawa, don zama dan Kasuwa a wani bangare na kasuwancinsa na hada sinadarai a kamfanin (Nasibi Pest Control Enterprises Kula).  Ya yi aiki a matsayin manajan tallace-tallace.
 Ba da dadewa ba, ya sake komawa makaranta don karatar Mass Communication a Jami’ar Bayero, Kano, inda daga nan Badamasi Burji ya halarci Cibiyar Alazhar (ALIYU IBN ABI Talib Kano, daga 1986 zuwa 1987) don karatun addini.
 Ya yi aiki tare da makarantar Danfodio Islamiyya a matsayin malami kuma mai taimaka wa Mamallakin makarantar, Malam Mahmud Aliyu Mahmud daga 1987 zuwa1999. Bayan haka, ya shiga harkar kasuwanci ta hanyar shiga kamfanin Nagari General Enterprise, babban kamfanin gas din girki Wanda yake gudanar da harkokinsa a Kano Ya yi aiki a matsayin babban akawu, kuma bajintar da ya nuna ya sa ya rike mukamin manajan darakta.
 A matsayina na dan jarida kuma mawallafi nayi mamaki lokacin da na ziyarci kauyen Burji kuma na ga ayyukan alheri da Alhaji Badamasi Burji ke gabatarwa ga jama’arsa wadanda mafi yawa Cikin Masu hali basa taimakawa al’ummar da suka taso a Cikin su Wanda yin hakan Yana da muhimmanci sosai a wannan zamanin.
 Da wuya na yi rubutu a kan wani Mai hali don kawai in yaba shi ko in yaba wa abubuwan da yake, amma abin da Badamasi Burji ke yi ya cancanci a buga masa gangar don wasu su yi koyi da shi.
 Ilimi….
 Alhaji Badamasi Burji shi kadai ya gina makaranta a garin sa wanda a yanzu haka yake daukar yara dari ake koya musu karatu kyauta, kayan makaranta kyauta da kuma ciyarwa a lokutan makaranta, ina ganin wannan wata alama ce da ta cancanci girmamawa.
 Tallafin Sana’o’i….
 Alhaji Badamasi ya tallafawa dubun dubatan mata da matasa daga Garin Burji da makwabta kuma har yanzu ana ci gaba da shirin karfafa musu gwiwa don su zamo Masu dogaro da Kai.
 Alhaji Badamasi Burji shi ne Wanda ya assasa Badamasi Burji Foundation, wacce aka kafa a shekarar 2015.
 Ya fara ne da daukar nauyin kafa makarantar firamare da sakandare ta musamman ta Islamiyya da ta Yamma a yankin tare da kimanin yara 5,212 da ke karatu a halin yanzu tare da isharar neman ilimi kyauta, kayan makaranta kyauta, ciyarwa kyauta, littattafai kyauta da kayan rubutu.  Karatu cikin yanayi mai kyau tare da wadatattun ajujuwa.  Ta dauki nauyin dalibai 109 ‘yan mata 98 ​​da yara maza 11 zuwa makarantun sakandare daban-daban.
 An kuma kirkiro shirin tallafawa yara mata da nufin horar da ‘yan matan a kan sana’o’i daban-daban da nufin su zama masu dogaro da kai.  Shirin da aka gabatar bayan shirin karfafawa gwiwa shi ne rage kwarar da mazauna karkara keyi zuwa cikin birane, samar da aikin yi, dogaro da kai da kuma samar da dama ga al’umma don inganta ci gaban zamantakewar al’umma da yankin Mahaifarsa ta Burji.
 Matan an riga an basu horo kan sana’oi daban daban wadanda suka hada da yin sabulu, kayan kwalliya, dinki da sauransu.  Kashi na biyu na shirin karfafa gwiwa zai fara aiki nan bada jimawa ba.
 Gidauniyar ta dauki gabarar shuka bishiyoyi kyauta don inganta yanayi da hana kwararar hamad Waɗanda suka haɗa da fa’idodin zamantakewar jama’a, muhalli da tattalin arziki ga al’umma.  A wani bangare na shirin duniya na sanya muhalli kore.  BBF ta ƙaddamar da Bishiyoyi 10,000 (Dubu Goma) waɗanda yaran makaranta, iyayensu da ɗaliban cibiyar ilimin manya za su yi.
 A yau, yanayin ilimin a Makarantun gwamnatin a jihohi da yawa a yankin ya na samun tasgaro sosai.  Yawancin makarantu a nan ba su da ƙwararrun malamai da kayan koyarwa, duk da cewa gine-ginen makarantu sun lalace matuka.  Kuma cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a tsakanin Shugabanin a fannin ilimi, waɗanda suka gwammace tura ya’yansu da Yan uwansu zuwa makarantu masu zaman kansu.
 Alhaji Badamasi Burji mutum ne mai taimakon jama’a, Mai karamci kuma mai matukar tausayin mutane, kaunarsa ga jama’arsa ce ta tilasta min rubuta wannan Labarin.
 Allah ya sakawa Alhaji Badamasi Burji da alherinsa, kuma ya Bamu irinsa da yawa a cikin al’ummominmu.