December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Nan da Kwana 4 masu zuwa Zan Kawo Karshen Yan Bindiga a Zamfara – Gwamna Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara ya lashi takobin murkushe ‘yan bindiga cikin kwanaki hudu tare da kawo karshen muggan ayyukansu a fadin jihar Baki Daya.

Gwaman Bello Matawalle Muradun ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakwancin shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC kuma Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da takwaransa na Jigawa Abubakar Badaru a wata ziyarar jaje da suka kai Gusau Babban Birnin jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya gargadi ‘yan bindiga a jihar da su tuba ko su sauya sheka domin ya tsara sabon tsarin yadda zai tunkari matsalar kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Ya ce dakatarwar da ya yi wa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda mu’amala da ‘yan ta’adda somin tabi ne, yana mai cewa a cikin kwanaki hudu masu zuwa, zai shawo kan duk wadanda ke sanya rayuwar al’umma da basu ji ba basu gani ba cikin kuncin rayuwa.