December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Rasuwar mahaifiyar Sarakunan Kano da Bichi Babban rashi ne ga Kasa baki daya – Sen. Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Dr. Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana Rasuwar mahaifiyar Masu Martaba Sarakunan Kano da biya a Matsayin Babban rashi ba ga Kano Kadai ba har da Kasa baki daya.

Sanata Shekarau ya bayyana hakan ne Cikin wani Sako daya wallafa a shafukansa na dandalin sada Zumunta.

Innalillahi wa Inna Ilaihir Raji’un

“A safiyar Wannan Ranar ta Asabar 12 Ramadan,1442AH muka tashi da rasuwa uwa a gare mu Hajiya Maryam Ado Bayero (Mai Babban Daki) Mahaifiya ga Maimartaba Sarkin Kano da Sarkin Bichi”. Inji Sanata Shekarau

“Ina mika Sakon ta’aziyya ga yan uwa Sarakunan kano da Bichi da zuri’ar Marigayi Alh Dr Ado Bayero da Al’umma kano baki daya. Allah ya jikan ta ya bata Aljannah madaukakiya Amin.”