Tsohon Sarkin Kano Muhd Sanusi II ya Mika ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Sarakunan Kano da Bichi

Date:

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya aike d sakon ta’aziyyarsa na mutuwar Hajiya Maryam Ado Bayero ga al’ummar jihar Kano baki daya.

A wani bidiyo da yake yawo a dandalin sada zumunta na zamani, wanda aka saka shi a shafinsa Mai Suna Muhammadu Sanusi II Wanda ya yi magana game da babban rashin da aka yi a Kano.

Da yake jawabi a Bidiyon, Malam Sanusi II ya ce: “Yau mun tashi da rasuwar mahaifiyarmu, Maryam Bade (Ado Bayero), uwargidar marigayi Sarki Ado Bayero.”

Mai martaban ya cigaba da cewa: “Ta rasu a kasar Masar, mu na mika ta’aziyya ga daukacin al’umma.”

A wannan bidiyo da aka wallafa a shafin Muhammadu Sanusi II ya yi wa marigayiyar addu’a tare da sauran jama’a.

“Allah ya sa ta huta, Allah ya sa ciwon da ta yi ya zama kaffara.” Sanusi ya ke cewa za ayi rashin mahaifiyar magajinsa da kuma Sarki Nasiru Ado Bayero.

Malam Sanusi II wanda ya bar karagar mulki a bara ya sa an yi wa marigayiyar salatin Annabi SAW kafa 10 da karatun suratul Ikhlas domin ta samu ceto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...