December 9, 2021

KADAURA 24

Inuwar sahihan labarai

Yanzu-Yanzu :Ganduje ya Kona Gurbattatun kayiyakin da Hukumar Kare Hakkin Masu siyayya ta kwace

Daga Siyama Ibrahim Sani

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullah Umar Ganduje ya jagoranci kone kayiyakin miliyoyin Nairori d Hukumar Kare Hakkin Masu siyayya ta jihar Kano ta Kama a wasu daga Cikin Kasuwannin jihar Kano.

Yayin da yake jawabi Gwamna Ganduje yace gwamnatin jihar Kano bazata yi Kasa a gwiwa ba wajen cigaba da taimakawa Hukumar domin ta cimma nasarar da ake fata.

Ganduje yace gwamnati ta damu sosai da yadda ake Sayarwa al’ummar jihar Kano Gurbattatun kayiyaki wadanda suke da ke cutar da lafiyar al’umma.

” Saboda muhimmancin Wannan aikin yasa gwamnatin jihar Kano ta dauki Ma’aikata Kuma muke basu Gudunmawar data dace domin su sami nasarar aikin su”. Inji Dr Ganduje

Gwamna Ganduje ya bada tabbacin cigaba da Baiwa Hukumar goyon baya domin magance Masu sayar da Gurbattatun kayiyaki da Kuma wadanda suke sayar da kayan da wa’adinsu ya Kare.

A Jawabinsa shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu siyayya ta jihar Kano Baffa Babba Danagundi yace sun Kama kayiyakin miliyoyin Nairori a Kasuwannin jihar nan.

Kadaura24 ta rawaito cewa Baffa Babba ya yabawa Gwamna Ganduje bisa irin gudunmawar da yake Baiwa Hukumar tare kuma da yadda Gwamnan yake Baiwa Hukumar kayan aiki domin Inganta aiyukansu.