Kansilolin 11 daga karamar hukuma daya sun fice daga jam’iyyar APC a Kano

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

Zababbun Kansilolin 11 na karamar hukumar Sumaila sun bayyana ficewarsu daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP Mai kayan marmari bisa wasu dalilai da suka zaiyana.

Cikin wata wasika mai dauke da kawanan watan 04 ga watan Janairu 2023 kansilolin su 11 sun ce sun bar jam’iyyar ne saboda rashin girmama su da Shugaban karamar hukumar ke yi.
Talla
Wasikar Mai dauke da sa hannun dukkanin kansilolin sun ce Shugaban karamar hukumar ta Sumaila yana tsangwamar su tare da yin halin ko un kula da lamarin su.
” Mu kansilolin karamar hukumar Sumaila mu goma Sha daya 11 na mazabu 11 mun fita daga jam’iyyar APC mun koma jam’iyyar NNPP, sakamakon tsangwama da halin ko in kula daga shugaban karamar hukumar Sumaila da Kuma da Kuma wulakanta yan jam’iyyar na mazabun mu”.
Talla

Kansilolin da suka hanya hannu akan wasikar dune Shugaban kansilolin Mustapha Garba Haladu (Council Leader), Umar Ibrahim Umar mataimakin Shugaba , Nuhu Ado Gala Shugaban masu rijaye da kuma mai tsawatarwa a majalisar kansilolin Abubakar Ahmed .

Sauran kansilolin sune Isma’il Sabi’u Salisu, Ibrahim Abubakar, Ma’amiru Nuhu, Atiku Idris, Umar Abdulsalam, Sule Adamu, and Danjuma Saleh.

Ga wasikar da suka rubuta

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin...

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...