Daga Auwalu Alhassan Kademi
Ana zargin wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano da illata wani jariri ɗan kawanaki biyar.
Likitan dai ya bar tsirkiyar da ya ɗaure hannun jariri da ita yayin daukar jini har tsawon awanni 18.
Wanna ne ma ya jawo hannun yaro ke neman rubewa a halin yanzu.

binciken da wakilin Premier Radio ya gabatar ya gano cewa an yiwa mahaifiyar yaron aikine aka ciro shi daga cikinta.
Daga bisani likita ya ce yana fama da matsalar numfashi da hakan ta sa tilas aka kwantar dashi a bangare jarirai.
an kuma yi zargin cewa, awa 18 ba wani daga cikin jami’an lafiya a asibitin da ya kula yaron, balle ya lura da ɗaurin dake hannunsa, har sai da mahaifiyarsa taje bashi mama.

Tuni dai wasu likitoci suka ce sai dai a yanke hannun wanna jariri, sakamakon shafe tsahon lokaci jini bai gindaya ba.
Sai dai mahaifin yaron Malam Umaru Shamsu ya ce ma’aikatan asibitin na nuna masa wulakanci duk da dattakon da ya nuna.
Ya ce ya yi mamaki da aka kirashi wai yaje ya siyo maganin da za a baiwa ɗan nasa a ranar Litinin, duk da ɗanyen aikin da aka yi masa.
Kadaura24 ta tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta Asibitin na Malam Aminu kano don jin yadda Akai aka haihu a ragawa, Amma ta ce mu bata lokacin zata bincika tare da sanar da mu abin da ta binciku, za dai mu cigaba da bibiyar lamarin.