Fashewar tayar wata babbar mota ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 5 a Kano

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Wani hatsarin mota yayi sanadiyyar rasuwar mutane da biyar, inda wasu Kuma suka hadu da munanan raunika a kano.

 

Hatsarin dai ya afku ne a jiya Asabar, a kan titin kano zuwa zaria a dai-dai garin yadakwari dake yankin karamar hukumar Kura, inda wata babbar motar daukar dakon mai talakume wasu motoci guda biyu Wanda da ke cike tab da mutane.

 

Kadaura24 ta rawaito akalla ba a kasara ba kimanin mutane biyar ne suka rigamu zuwa gidan gaskiya nan take, yayin da wasu kuma suka da dama suka jikkata.

 

Talla

Wakilin mu wanda lamarin ya faru aka idon sa yace tuni dai Jamian hukumar kiyaye afkuwar haduwa ta kasa reshan jahar kano sun garjaya da marasa lafiyar zuwa asibiti don basu agajin gaggawa.

 

Shaidun gani da idon sun bayyana was wakilin namu cewa hatsarin ya faruwa ne sakamakon fashewar tayar daya daga cikin tayoyin gaba na babbar motar wanda hakan tasa direban ya kasa sarrrafa motar yadda ya dace, Kuma har ya je ya buji wadancan motoci guda biyu.

 

Mun yi kokarin Jin ta bakin jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa, bayan mun yi magana da babban jami’in hukumar dake kula da yankin da lamarin ya faru Labaran Abdullahi, yace mu bashi dama zai bincika, Amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahotannin bamu ji ba, Inda ya magantu da mu kawo muku .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...