Yan Sanda a Jigawa sun kama matar da ta binni jaririn da ta haifa

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

 

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta ce jami’anta sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da ke ƙauyen Tsurma a ƙaramar hukumar Kiyawa bisa zargin binne sabon jaririn da ta haifa a ban ɗaki.

 

Yayin da yake tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Lawan Shiisu Adam ya ce sakamakon bayanan sirrin da rundunarsu ta samu ne ya kai su ga gano matar tare da tono jaririn a ban ɗakin gidan.

 

”Bayan haihuwar ta ne sai ta shiga ban ɗaki ta haƙa rami a kusa da masai ta binne jaririn”

 

Talla

Ya ce bayan tono jaririn ne aka garzaya da shi babban asibitin Dutse inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu.

 

DSP Shiisu Adam ya ce matar ta sanar da su cewa ta samu cikin ne ba ta hanyar aure ba, ta kuma bayyana wani saurayinta mai suna Ahmadu Sale wanda aka fi sani da ‘Dan kwairo’ da ta ce shi ne ya yi mata cikin,.

 

Kawo yanzu dai matar mai shekara 30 tare da saurayin nata mai shekara 25 suna hannun jami’an ‘yan sanda.

 

Tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun zuwa shalkwatar cibiyar binciken manyan laifuka ta rundunar da ke babban birnin jihar Dutse.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...