Satar Mutane: Mutanen Zaria da Ido Daya suke barci – Sarkin Zazzau

Date:

Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ya ce birnin Zariya na cikin tsaka mai wuya.

Sarkin ya bayyana hakan ne a yau Litinin lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Shugabannin Tsaro ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samueal Aruwan.

Sarkin ya ce mazauna barnin ba sa samun barci da ido a rufe saboda sace-sacen mutane da ake yin don neman kuɗin fansa a cikin birnin da kewayensa.

Ya bayyana yanayin a matsayin wanda ba za a amince da shi ba, tare da yin kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Alhaji Bamalli ya ce duk da cewa akwai cibiyoyin tsaro kamar makarantar horar da sojoji a yankin masarautar tasa, amma al’ummarsa na zaune cikin fargaba.

Shi kuwa Kwamishina Aruwan cewa ya yi sun je fadar ne don ƙara ƙwarin gwiwa tare da jajanta wa masarautar kan harin da aka kai Makarantar Koyon Fasaha ta Nuhu Bamalli da kuma wasu al’ummomin maƙwabta.

Ya ce gwamnati na yin bakin ƙoƙarinta don kare masarautar da jihar baki ɗaya.

174 COMMENTS

  1. Бій Усик – Джошуа пройде 25 вересня в Лондоні на домашній арені англійського футбольного клубу “Тоттенхем”. Читайте також: Усик вважає бій з Джошуа головним у своєму житті – промоутер . Усик Джошуа смотреть онлайн Кращі моменти бою (ВІДЕО) Олександр Усик. Тренер Пітер Фьюрі каже, що Ентоні Джошуа ніколи не обирав собі слабких опонентів. “Ентоні Джошуа проти Олександра Усика – це відмінний бій у

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...