Makarantar S.A.S Ta Bada Gagarumar Gudunmawa a Rayuwar Mu – Abdullahi Maikano

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Tsohon shugaban gidan Radiyon Nigeria Shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan Alhaji Yahaya Abdullahi Maikano ya ce makarantar koyar da harshen larabci ta SAS ta bayar da gagarumar gudun mowar a rayuwar su wacce baza su taba mantawa ba.

 

Alhaji Yahaya Maikano ya bayyana hakan ne lokacin da kungiyar tsofaffun daliban makarantar ‘yan Aji na shekarar 1980 zuwa 1981 ta karrama shi bisa nasarorin da ya samu a rayuwa da kuma irin gudun mowar da yake bayarwa a cigaban makarantar ta SAS.

 

Ya ce an koya musu ilimi da tarbiyya da girmama na gaba da kuma jajircewar a karatu wanda hakan ya bada gagarumar gudun mowar a rayuwar su.

Talla

Abdullahi Maikano ya ce mafi yawan kananan laifuffuka da ake akatawa a tsakanin al’umma musamman Wanda ya hada da matasa yana samo asalin ne sakamakon abin da yara suke koya a cikin wayoyin su.

 

Daga nan ya bukaci iyaye da su mayar da hankali wajen neman ilimi domin cigaban rayuwar su, ya na mai cewa akwai bukatar iyaye su rika Sanya idanu akan wayoyin ‘ya’yan su domin gudun aikata abubuwan da basu dace ba.

 

Wadanda aka karrama din sun hadar da Farfesa Umar Sani Fagge da Farfesa Umar Muhammad Labdo da Farfesa Shehu Ahmad Fagge da Alhaji Yahya Abdullahi Maikano Marmara da Dakta Bashir Ibrahim Fagge da Dakta Saidu Zaria da Alkali Kabir imam da kuma Abubakar Haruna Khalil.

 

Da yake jawabi a yayin taron, Farfesa Umar Sani Fagge ya bayyana takaicin sa kan yadda Yara a yanzu basa jajircewa suna karatu sai dai kallace-kallace a wayoyin hannu wanda hakan yake sa su koyi sabbin dabi’u.

 

Taron ya sami halartar manyan Alkalai da shugabanni ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...