Kungiyar Masu fito ta Sauke Shugabanta na Shiyyar Sokoto

Date:

Daga Ibrahim Sidi Jega

Kungiyar Masu fiton kayiyaki Shiyyar jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara ta sauke Shugaban rikon kwaryar Kungiyar Alhaji Aminu Dan Iya Saboda Wasu dalilai guda 3 .

Mai Magana da yawun Kungiyar Alhaji Sanusi Na Allah Olumbo shi ne ya bayyana hakan ga Manema labarai Cikin su har da

Alhaji Sanusi Na Allah yace Shekaru 6 kenan Aminu Dan Iya yana rikon kwaryar Kungiyar ba tare da ya shirya Zabe Wanda yace hakan ya Saba da yarjejeniyar da aka yi dashi.

Yace Kuma Dan Iyan ya Gaza Kare musu Hakkokin su duk da kwakarin da Shugaban Hukumar Hana fasa kauri ta Kasa Kanal Hamid Ali Mai Ritaya na tausayawa ‘ya’yan Kungiyar wajen basu damammaki, Amma Dan iya yana rufda Cikin akan damar wajen Gina kansa.

Mai Magana da yawun Kungiyar Masu fiton yace Suna Zargin Aminu Dan Iya yana haɗa Baki da Wani kwantirola a yankinsu wajen aikata abubuwan da basu kamata ba, Inda har aka baiwa Dan iyan Ofis a ofishin kwastam Wanda haka ta bashi Dama yake Hana kowa aikinsu in bashi Dan iyan ba.

Ya Kara da cewa Wadancan dalilai ne suka sa suka sauke shi Daga Kan mukamin nasa tare da rokon gwamnatin Tarayya da Shugaban Hukumar Hana fasa kwauri ta kasa Kanal Hamid Ali dasu kawowa Kungiyar Dauki ta Hanyar basu damar gudanar da Zabe.

Alhaji Sanusi olumbo yace bayan cire Tsohon shugaban rokon kwaryar Kungiyar yanzu sun nada Alhaji Ibrahim Milgoma sokoto a Matsayin mai rikon kwarya Kuma zai shirya Zabe nan da Wata Mai zuwa .

Daga Karshe dai ance kowanne Dan Kungiyar Yana da damar shiga zaben har da tsahon Shugaban, sannan kuma zasu kalubalanci tsahon Shugaban a kotu don bin kadin Hakkokin su.

Da yake akwai Zargi a lamarin Hakan tasa Muka tun tubi Tsohon shugaban Kungiyar Masu fiton kayayyakin Alhaji Aminu Dan Iya don Jin yadda akai aka haihu a ragaya Kan Wannan lamari, sai dai mun kirawo wayarsa Bata Shigaba Amma mun aika Masa sakon karta Kwana, Amma har lokacin haɗa Wannan rahoto Bai kirawo muba.

56 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...