Daga Ibrahim Abubakar Diso
Dan majalisa tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gwale a jihar kano Hon. Abdullahi Lawan kenken ya yi alkawari gudanar da aikin hanyar data tashi daga gidan masu larurar kwakwalwa na Yamadawa Dorayi wanda yabi ta Tunga har zuwa iyakar Gwale da karamar hukumar Kumbotso a kano.
Alh Lawan kenken ya bayyana haka ne yayin da yake kaddamar da aikin titi a unguwar sani mainagge da ke Kano.
Sanin aiki da kwazo su ne ginshikin shugabanci – daga Aminu Dahiru
yace wannan hanya tana cikin hanyoyin da suke ci masa tuwo a kwarya , ya kara da cewa yasha bada gudunmawa ana zuba kasa ana yin ciko a wannan hanya, don haka da izinin Allah za ayi wannan titi nan bada dadewa ba.
Da zarar na zama gwamnan kano zan biya yan fansho hakkokin su – Dan takarar PRP
Yana mai cewar ma’aikatar kula da zai-zayar kasa ce zata gudanar da wannan aiki.
Al’ummar yankin sun dade suna kokawa da yadda hanyar ta lalace, babu shakka idan aka gudanar da aikin zai taimaka sosai wajen fitar da mutanen unguwar daga mawuyacin halin da suka dade a cikin.