Da zarar na zama gwamnan kano zan biya yan fansho hakkokin su – Dan takarar PRP

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Dan takarar Gwamnan jihar kano a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta biyan yan fansho hakkokinsu da zarar yayi nasara a babban zaben shekara ta 2023.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin jaridar Kadaura24 a ofishinsa dake nan kano.
Dan takarar ya bayyana cewar alamarin fansho abu ne da yake bukatar kulawa ta musamman, duba da cewa ma’aikata sun kan kare rayuwar suna hidimtawa gwamnati da al’umma, akwai bukatar a basu hakkokinsu, Wanda zasu ne zasu cigaba da tafiyar da al’amuran rayuwar su.
Ya kuma nuna damuwar sa dangane da yadda gwamnatin da ta gabata tayi amfani da kudaden yan fansho wajen gine-ginen da ba zai amfani yan fansho ba, Sannan gwamnati mai ci ta gaza warware matsalar wanda sanadiyar hakan kudaden suka taruwar da aka kasa biyansu hakkokin nasu.
Yakasai ya kara da cewa idan Allah ya bashi nasara a babban zaben shekara ta 2023, zai zo da sabbin tsare-tsaren da ba sai an ciyo basusuka ba don gudanar da wasu ayyukan.
Talla
Yace cin bashi ba laifi bane idan za’a yi amfani da kudaden wajen yin ayyukan da zasu gina al’umma, tun da dama daga manyan kasashen duniya ma suna cin bashi wanda dashi suke gina alummar su, don haka ba laifi bane ciyo bashi matsalar ita ce yadda za’a kashe kudaden.
Kazalika Ya bayyana cewar idan gwamnati zata kulla yarjejeniya da kamfanoni masu zaman kansu ta kuma Samar musu da yanayi mai kyau Zasu iya Samar da managartan tsare tsare da ayyukan da ba sai gwamnati ta shigo ciki ba, Wanda ba sai gwamnati ta je ta ciyo basusuka ba.
Dangane da tabarbarewar ilimi kuwa dan takarar ya bayyana cewar gyara harkokin ilimi tun daga matakin firamare shi ne zai magance tabarbarewar ilimi a jihar Kano, kasancewar bangaren ilimi ba abu ne da za’a taba shi sama sama ba ne, kasancewar ba aiki ne da ido zai iya gani ba kamar aikin gadar sama .
Don haka ya ke baiwa al’ummar jihar nan tabbacin cewar idan har sukayi nasara a babban zaben shekara 2023 Zasu gyara harkokin ilimi tun daga tushe Wanda zai taimaka wa dalibai damar cin jarabawa har zuwa matakin jami’a.
Daga karshe yayi kira ga yayan jam’iyyar da jagororinsu da su saki jikinsu su tunkari al’umma su nemi hadin  kansu tare da wayar musu da Kai kan cewar Su suke da damar cin zabe a jihar nan don baiwa masu jini a jika damar jagorancin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku duniya ta ke yayi, dole mu hada kai wajen yada manufofin gwamnatin Kano – Waiya ga yan jaridun yanar gizo

  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na hada kai...

A karon farko bayan cire shi daga sakataren gwamnatin Kano Baffa Bichi ya Magantu

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr....

Gwamna Yusuf ya biya biliyan 16 ga yan fansho a Kano

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada...

Dr. Danmaraya Ya Fara Shirin Sauya Fasalin Ma’aikatar Kudi ta Kano

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan harkokin kudi na jihar Kano,...