Daga Abubakar Sadeeq
Amb. (Dr). Yunusa Yusuf Hamza Falakin Shinkafi ya bukaci al’ummar dasu rika girmama mata ta hanyar daina yi duk wani nau’i na cin zarafin ‘ya’ya mata.
Dr. Yunusa Yusuf ya bayyana hakan ne lokacin da ya gabatar da makala yayin Wani taron da aka shirya domin wayar da kan al’umma game da illar cin zarafin ‘ya’ya mata da Kuma muhimmanci kula da wadanda abun ya faru da shi a makarantar firamare ta Rimi City dake unguwar Yakasai a birnin Kano.
Falakin Shinkafi wanda yake guda ne cikin wadanda suka gabatar da makala a yayin taron, ya yi bayani Mai tsahon dangane da matsalolin da mata suke fuskanta a ko’ina a duniya duk kuwa da yawa da muhimmanci da suke da shi a cikin kowacce al’umma.
” Yanzu haka bincike ya nuna mata suke da kaso 45.58 cikin dari Kuma a ko Ina a duniya an gamsu cewa mata muddin aka basu dama zasu bayar da gudunmawa mai yawa wajen cigaban al’umma, Amma a Maimakon hakan sai ake bigewa da cin zarafin su wanda hakan ba dai-dai bane”. inii Falakin Shinkafi
Masarautar Kano tana bayar da gagarumar Gudunmawa a bangaren Lafiya – Sarkin Kano
Dr. Yunusa Yusuf yace akwai nau’ikan cin zarafin ‘ya’ya mata da ake yi yanzu da suka kai kusan guda 5 dukkanin su suna taimakawa wajen mayar da hannun agogo baya, wajen kokarin da ake na magance matsalar cin zarafin ‘ya’ya mata.
” Mata iyayene Kuma su ake aura a sami nutsuwa, sannan su suke baiwa wanne irin mutum tarbiyya har yakai Inda yake, Amma duk da aka ba’a basu damar su bada gudunmawaisu ta fuskar inganta tattalin arzikin kasa, harkokin Siyasa da Ilimi da dai sauran su”. A cewar Dr. Yunusa Yusuf Hamza
Ganduje yace dole doka ta yi aiki akan dan Chinan da ya kashe Ummita
Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya gabatar da makalar ne Mai taken ” Yadda za’a fahimci alfanu da damammakin da suke cikin bin dokokin hana zarafin ‘ya’ya mata da gudunmawarsu wajen ciyar da kasa gaba”