Sarkin Kano ya nada Sheikh Daurawa a matsayin babban limamin jami’ar Skyline

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

A safiyar jiya Alhamis ne, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya naɗa babban malamin addinin Musuluncin nan, Assheikh Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, a matsayin babban limamin sabon masallacin jami’ar Skyline da ke tsohon ginin dogon bankin a kusa da sakatariyar Audu Baƙo da ke Kano.

 

Bikin naɗin da aka yi shi a fadar Mai Martaban ya samu halartar manyan jami’ai na fadar Mai Martaba San Kanon.

 

Sarkin Kano ne yake gaisawa da sheikh Daurawa

Daga isar shi fad’ar, Sheikh Malam Aminu Daurawa ya zarce ya gaida sarki, sannan ya yi wa sarki addu’ar fatan alheri da fatan zaman lafiya ga al’ummar jihar Kano, da ma ƙasa bakiɗaya.

Talla

A wani abu da ba a saba gani ba a fada sosai, sarkin ya buƙaci su gaisa da malam Daurawa, inda kuma ya yi addu’a ta musamman tare da yabawa Shehin Malamin game da ƙoƙarin wayar da kan mutane zuwa ga tafarkin Allah.

 

“Muna ganin irin abubuwan da malam yake yi na wayar da kan al’umma da nusarwa. Muna yi wa Malam godiya da addu’ar fatan alheri. Muna ganin bidiyoyi na karatuttuka iri-iri, Allah Ya saka da alheri.” Inji mai martaba sarki.

Talla

Haka kuma bayan an naɗa Malam tare da na’ibansa guda uku, a masallacin fadar Sarkin Kano, tawagar Malam Aminu Daurawa sun dawo domin sake yi wa mai martaba sarki addu’ar fatan alheri.

 

A karo na biyu bayan naɗin, sarki ya ce a gaya wa Malam Aminu Daurawa lallai malafar da aka ɗora masa ta dace kuma ta yi kyau. Wannan ya sa aka yi dariya tare da murna a cikin fadar ta Kano.

Sai da Sha’aban Sharada ya Amince da dokokin mu kafin mu bashi takarar ADP – Amb. Tasi’u Abdulrahman

 

TDRHausa ta rawaito bayan an naɗa wa Sheikh Daurawa rawani, an sanya masa alkyabba, sannan aka sanya masa malafa aka ba shi sanda, sannan kuma aka yi masa addu’ar fatan alheri.

 

Sauran waɗanda mai martaba sarkin ya naɗa, a matsayin na’iban Malam Daurawa sun haɗa da Dr. Jamilu Lawan Ajiya Fagge, daga jami’ar DutsinMa, a matsayin na’ibi na ɗaya. Sai Malam Anas Muhammad Madabo, a matsayin na’ibi na biyu. Sai kuma Dr. Muhammad Sulaiman Abdullahi, daga jami’ar Bayero, a matsayin na’ibi na uku.

Zamu yi amfani da Matasa a yakin neman zabe, amma ta hanyar da ta dace – Shugaban PRP na Kano

A lokacin da ake karanta takardar babban limamin Kano a bisa gwajin da aka yi wa Sheikh Daurawa da na’iban nasa, Farfesa Emeritus Sani Zahraddin ya bayyana cewa lallai Malam Aminu Daurawa yana ƙoƙari wajen faɗakar da al’umma da kuma nusar da su zuwa kan hanya tagari.

Sai dai a yayin jawabin farfesan, ya nemi malam da ya ja hankalin limamin masu tsawaita sallar Juma’a, har a yi minti 40 ko ma sama da haka ana huɗuba. Ya bayyana cewa lallai mafi kyawun zance shi ne wanda aka yi shi ɗan kaɗan, kuma ya zamo mai tarin ma’ana. Sannan ya ƙara da cewa ya kamata limamin su sani, a cikin masu bin su salla, akwai masu rauni da marasa lafiya da masu wasu buƙatun na daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...

Mun gano yadda yan Bauchi ke mamaye dazukan Kano – Gwamnatin Kano

Daga Nazifi Dukawa     Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano...