Gwamnatin Kano ta magantu kan zargin za ta sayar da gine-ginen kotu

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Kwamishinan shari’a, Musa Abdullahi Lawan ya ce babu wani shiri da gwamnatin Kano ta yi na sayar da wasu kotunan shari’a a jihar.

 

Wasu Lauyoyin da ke Kano ne dai su ka garzaya wata babbar kotun Kano, suna neman ta hana gwamnatin jihar ɗaukar wani mataki a kan gine-gine da harabar kotunan.

 

Kotunan da abin ya shafa sun haɗa da Babbar Kotun Shari’a ta Gidan Maitasine, Ƴan Awaki, Kotun Shari’a ta Ƴan Alluna, Kotun Shari’a ta Shahuci, da Kotun Shari’a ta Goron Dutse.

Ganduje zai gabatar da kasafin kudin shekara ta 2023 wata mai kamawa ga majalisar dokokin Kano

 

Sauran sun haɗa da Babbar Kotun Shari’a ta Kasuwar Kurmi, da Kotun Shari’a ta Filin Hockey.

 

Da yake mayar da martani, Lawan, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Ayyuka kan Sauya-fasali da Ci gaban Kaddarori na Jihar Kano, ya ce ikirarin da lauyoyin su ka yi karya ce, maras tushe da siyasa da kuma ƙin gaskiya.

 

Abdullahi Lawan ya ce: “Gwamnatin jihar ba ta da shirin sauya wa Kotun Shari’a ta Goron Dutse da Kotun Shari’a Filin Hockey, Hausawa waje.

 

Talla

“Hukuncin da gwamnatin jihar ta yanke na mayar da Kotun Shari’a ta Ƴan Awaki ya faru ne saboda tashar motar Kofar Wambai ta matso har jikin ginin kotun.

 

“Bai kamata a zauna a kotun ba idan akwai hayaniya gami da karar motoci ko wani abu da zai ɗauke hankalin alkali da jami’an kotu da kuma masu ƙara.

 

“Kotu tana bukatar yanayi ns natsuwa don gujewa tabarbarewar shari’a.

 

Talla

“An mayar da Kotun ƴan Awaki ta koma titin Sabuwar BUK, inda ta kasance sashen kotunan shari’a gaba ɗaya da suka haɗa da, kotun shari’a, babbar kotun shari’a ta da kotun ɗaukaka karar shari’a da za a kammala a karshen watan Satumba. 2022, “in ji shi.

 

Lawan ya ce sauran kotunan Shari’ar na Kasuwar Kurmi da Ƴan alluna duk sun yi cikin kasuwa da yawa kuma ana samun hayaniya yayin yin Shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...