Jam’iyyar PRP zamu zo da sabon salon yaƙin neman zaben Gwamna a Kano – Salihu Tanko Yakasai

Date:

Daga Shehu Sulaiman Sharfadi
Dan takarar Gwamnan jihar kano a jamiyyar PRP Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya jaddada aniyarsa ta Kai ziyara daukacin mazabun jiharnan domin sanin halin da suke ciki.
Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake nan kano.
Dan takarar wanda ake yiwa lakabi da Dawisu ya bayyana cewar shi kadai ne dan takarar da ya iya zagayawa kananan hukumomin jihar kano 44 domin sadar da zumunci da kuma neman tubarraki ga limamai da sarakunan gargajiya.
Talla
Tanko Yakasai ya kuma bayyana cewar ya fara siyasa ne tun sama da shekaru Ashirin baya, kuma da zarar an fara gangamin yakin neman zabe za’a ga salon siyasa Wanda ake yiwa lakabi da Namu-ba-irin-Nasu-bane kasancewarsa a matsayin wanda ya fara siyasa tun daga tushe.
Ya kara da cewar yanzu haka shirye shirye sun kammala wajen ziyarar mazabun jihar kano 484 domin sanin halin da suke ciki, wanda yace wannan shima salo ne da babu wata jamiyya da zata jure hakan a fadin jihar nan.
Talla
Kazalika Yakasai ya bayyana kadan daga cikin tarihin rayuwarsa wanda yace hakan na nuni cewar shi ba sabon shiga bane da harkokin mulki, inda ya zayyana cewar yayi aiki da gwamnatin Dakta Abdullahi umar Ganguje a matsayin mai bashi shawara kan harkokin yada labarai, ya kuma yi Daraakta janar na yada labaran gwamnan jihar Kano.
Yace yayi aikin jarida da gidan rediyon freedom, kana kuma ya kwashe sama da shekaru Ashirin yana tsayawa takara daban-daban wanda hakan ta sanya ya zama kwararren dan siyasa mai burin ya taimaki al’ummar jihar Kano musamman masu Karamin karfi .
Alhaji Salihu ya bayyana cewar salon da wannan siyasa ta zo dashi salo ne da ba a taba yin irin sa ba tun da aka fara demokaradiyya a fadin kasa Nigeria, kasancewar dogon zango da salon yake dashi wanda a baya, daga yin zaben fidda gwani cikin wata daya ko biyu sai kaga an fara gangamin yakin neman zabe, sai kuma babban zabe wanda yanzu bayan anyi zaben fidda gwani sai an dauki dogon lokaci kafin a fara gangamin zabe, yanzu kuma sai an kwashe watanni biyar zuwa shida kafin a gudanar da babban zabe, kamar yadda Sabuwar dokar zabe ta tanada.
 ” Wannan salon wata dama ce da muka samu domin zagayawa lungu da sako don wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da ganin an zabi nagartattun mutane ba masu son zuciya ba” . Inji Tanko Yakasai
Daga karshe ya jajantawa al’ummar jihar kano musamman wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ta shafa a wasu kasuwannin jihar kano, da kuma ibtilain rugujewar wani gini a kasuwar wayoyin hannu dake Beruit tare da fatan Allah ya kare aukuwar hakan anan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna...

Gwamnatin Kano ta bayyana sunayen unguwannin da aka sami gurbatacciyar Iska

    Wani rahoto na mako-mako kan yanayin lafiyar iska da...

Sallah: Gwamnatin Kano za ta hukunta gidan wasan da ya bar masu shigar banza da shaye-shaye

Daga Rahama Umar Kwaru   A kokarin ta na yaki da...

Sallah: Hussari ya sauke kabakin arziki ga yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwale

Daga Ibrahim Abubakar Diso   Tsohon Dan Majalisar wakilai da ya...