Yanzu-Yanzu:Bayan Rantsar da sabbin kwamishinoni, Ganduje ya bayyana ma’aikatun su

Date:

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci taron rantsar da sabbin kwamishinoni Kuma Yan Majalisar zartarwar ta jihar kano su guda 11, Inda Kuna ya bayyana ma’aikatun da zasu yi aiki.

Taron dai ya gudana ne a rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata a birnin Kano.
Yayin taron gwamna Ganduje ya ce ya zabo sabbin kwamishinonin ne bisa chanchantar su da Kuma kwarewar da suke da ita a harkokin na yau da Kullum, Inda yace yana sa ran dukkanin su zasu yi duk mai yiwuwa wajen ciyar da gwamnati da jihar kano gaba.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan ya kuma Kara da cewa yana fatan zasu yi amfani da kwarewar da suke da ita wajen Kawo cigaba a ma’aikatun da aka tura su, sannan su taimakawa gwamnati wajen kammala manyan aiyukan da ta faro kafin karewar Wa’adin gwamnatin.
Gwamna Ganduje ya bayyana sunayen sabbin kwamishinonin da Kuma ma’aikatun da aka turasu kamar haka:
1. Dr. Jibril Yusuf rurum – Ma’aikatar Noma
2. Ya’u Abdullahi Yan Shana – Ma’aikatar Ilimi
3. Alhaji Ibrahim Dan azumi Gwarzo – Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare
4. Abdulhalim Abdullahi Liman – ma’aikatar Raya karkara
5. Alh. Lamin Sani Zawiyya – Ma’aikatar kananan Hukumomin da Masarautu
6. Hon. Garba Yusuf Abubakar – ma’aikatar Ruwa
7. Hon. Adamu Abdu Panda – ma’aikatar kudi da cigaban tattalin arziki
8. Hon. Sale Kausani – ma’aikatar gidaje da sufuri
9. Alh. Ali Musa Hamza Burum-burum – Ma’aikatar kula da yawun bude idanu da al’adun
10. Dr. Aminu Ibrahim tsanyawa – Ma’aikatar Lafiya
11. Alhaji Kabiru Muhammad – Ma’aikatar Aiyuka na Musamman.
Gwamnan ya horesu da su zamo Masu himmatuwa da sadaukar da kai wajen sauke nauyin da aka dora musu, sannan ya taya su murna da su da iyalansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Sarki Sanusi Fadi Matsayarsa Kan Hawan Sallah Babba

Daga Sani idris Mai waya   Mai Martaba Sarkin Kano na...

Sallah: Shugaban K/H Rano ya gargadi matasan yankin kan zaman lafiya

Daga Isa Ahmad Getso   Shugaban karamar hukumar Rano Malam Naziru...

Kansila a K/H Garum Mallam ya rabawa marayu 300 kayan Sallah

Daga Safiyanu Dantala Jobawa   Sama da yara mayaru 300 ne...