Daga Rahama Umar Kwaru
Majalisar zartaswa ta jihar Kano ta amince tare da ba da umarnin yin alama tare da rushe duk wasu gine-ginen da aka gina a r Kwarin Gogau a cikin babban birni.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyanawa manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa na mako-mako, wanda aka gudanar a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnatin Kano.
Har ila yau, an bada umarnin rushe duk gine-ginen dake kan magudanun ruwa a ciki da kewayen Kasuwar Kantin Kwari da nufin kawar da duk wani abun da ke kawo cikas ga ruwan dake wucewa ta cikin kasuwar.
Bayan karbar rahotannin abubuwan da suka haifar da ambaliyar ruwa a kasuwar daga kwamishinnan ayyuka Engr. Idris Wada Saleh da na Muhalli, Dokta Kabiru Ibrahim Getso, majalisar ta kuma ba da umarnin a rushe duk wasu gine-gine na wucin gadi da aka a hanyar ruwa dake ciki da wajen kasuwar nan take.