Rushewar Gini: Hukumomin bada agaji na cigaba da aikin ceto a kasuwar waya ta Beruit

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da hukumar kashe gobara ta jihar kano da sauran jamian yansanda da alumma da dama na cigaba da kokarin tono mutanen da gini Mai hawa biyu ya ruftawa a kasuwar wayar hannu ta Berui dake Kano.

 

Al’umma da dama a cikin kasuwar suna ta alakanta abin da cewa son rai ne  daga cikin wasu shugabancin kungiyar kasuwar ya haifar da hakan.

 

Yanzu-Yanzu : Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon ruftowar wani gini a kasuwar Beruet dake kano

A wata ganawa da yayi da manema labarai jami’in hulda da jami’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Yusuf yace har yanzu ba’a kiyasce yawan mutanen da ginin ya danne ba, amma ana cigaba da ceto mutane tare da mikasu Asibiti domin samun kulawar likitoci.

Wakilin Kadaura24 wanda yanzu haka yake wajen da lamarin ya faru yace akan idonsa an sami nasarar ceto mutane 7 daga ciki da ransu.

 

NIMET ta yi hasashen samun ruwan sama mai karfi a jihohi 5 na arewacin Najeriya

Wakilin na mu yace yana ta kokarin jin ta bakin shugabancin kungiyar kasuwar amma hakan ya ci tura.

Zamu cigaba da Kawo muku halin da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...