2023: Umar Namadi Dan modi ya fi duk yan takarar gwamnan Jigawa Chanchanta – Garba Shehu

Date:

Daga Abubakar Sadeeq

 

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Jigawa Alhaji Garba Shehu wato magaji jahun garkuwa yace matukar al’ummar jihar suna bukatar jihar ta koma a Abar kwatance ta fuskar cigaba to basu da wanda ya dace su zaba idan ba dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC ba Alhaji Umar Namadi Dan modi.

Alhaji Umar Dan modi yanzu haka shi ne mataimakin gwamnan jihar Jigawa da shi aikin duk aiyukan alkhairin da Gwamna Muhd Badaru yayi, don haka dorawa akai bazai zamar masa Wani abu Mai wahala ba” a cewar Magaji garkuwa

 

Garba Shehu ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da wakilin Kadaura24 a jihar Jigawa a ranar Litinin.

 

Yace duk yan takarkarun gwamna a jihar Jigawa Babu Mai godewa da Ilimi Dan modi Saboda ya riƙe mukamai Masu tarin yawa Kuma a wurare da dama, hakan ce ma tasa gwamna Badaru yaga dacewar ya baiwa dan Modin takarar gwamna a APC ko za’a cigaba da dora jihar daga inda ya tsaya.

 

Akwai yiwuwar gwamnatin tarayya zata ciyo bashin Naira Tiriliyan 11a shekara ta 2023 – Ministar Kudi

“Ina so duniya ta Sani Umar Namadi Dan modi gogaggen ma’aikaci ne domin har manajan shiyya ya riƙe a Bankin Savana, ya kuma yi aiki a sashin kudi na kamfanin Dangote , sannan ya riƙe mukamin General Manager a hukumar kula da Inshora lafiya ta kasa, Kuma mamba ne a kungiyar Kwararrun akantoci ta kasa wato (ICAN), shi ne kuma shugaban kamfanin sarrrafa shinkafa na Danmodi , bata ga kwamishinan kudi da ya rike a Jigawa yanzu shi mataimakin gwamna tsahon Shekaru 8, kaga ko ai yasan harkokin tattalin arzikin fiye da kowa cikin yan takarkarun gwamna a Jigawa”. Inji Garba Shehu

Yace dama a shugabanci ana bukatar Mai Ilimi wanda yasan harkokin tattalin arziki domin da haka ne zai iya Kawo cigaba a Inda yake jagoranta, ba tare da an Sami matsala ba, Kuma babu wanda ya dace da Wadancan siffofi kamar mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi Dan modi.

NIMET ta yi hasashen samun ruwan sama mai karfi a jihohi 5 na arewacin Najeriya

” Badaru ya Kawo cigaba masu tarin yawan a jihar mu ta Jigawa, kamata yayi mu zabi wanda zai dora daga inda ya tsara domin da hakan ne kasashen da suka Cigaba har suka kai matakin da suka kai to haka muke bukatar jihar Jigawa ta ci gaba fiye da kowa yadda take a yanzu “. inji Magaji jahun

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Jigawa da su tsaya su yi karatun ta nutsu su zabi chanchanta don nemawa jihar Jigawa makowa ba a yanzu ba har anan gaba don anfanin ‘ya’yan mu da jikokinmu, Kuma duk cikin yan takarar mu Babu wanda yafi Alhaji Umar Namadi Dan modi Babu wanda ya fishi chanchantar zama gwamnan jihar Jigawa a shekara ta 2023.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...