Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin nemo Dan kwangilar da yayi aikin gina gadar Ado Bayero, dake Gyadi Gyadi wadda akafi sani da Gadar Lado.
Idan za’a iya tunawa kusan kimanin wata guda kenan da lalacewar wani sashi na gadar, wanda hakan yayi sanadiyyar ba’a bin hannu daya wata hannun da zai kai ka Na’ibawa.
Karamin ministan ma’aikatar ayyuka da gidaje Hon. Umar Ibrahim El-yakub ne ya bayyana hakan yayin da yake duba yadda aikin titin kano zuwa Zaria ke gudana a yau asabar.
Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi
“Wannan gadar tana da matukar muhimmanci ga al’ummar jihar kano dama baki da suke Shigowa jihar don haka ya zama wajibi dan kwangilar da yayi aikin ya dawo domin gyara ta don al’umma su cigaba da mararta”. Inji El-Yakub

Minista yace tuni ya bada umarnin a nemo dan kwangilar da yayi aikin gadar saman Ado Bayero dake daura da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin ya fara gyaranta.
” Cikin Wannan makon da Zamu shiga zaku ga anzi an gyara gadar sabods muhimmanci ta ga al’ummar jihar kano da Kuma harkokin sufuri da tattalin jihar kano da na kasa baki daya”.