Kishi: Wata Mata ta Kashe Tsohon Mijinta a Jihar Kebbi

Date:

Daga Umar Sani Kofar Na’isa

 

Wata mata Ƴar shekara 30 Mai suna Farida Abubakar ta kashe tsohon Mijin ta a garin birnin Kebbi dake jahar Kebbi a Nigeria.

 

A wani bayani da Rundunar Yan Sandan jihar Kebbi ta fitar ta hannun Kakakin ta Nafi’u Abubakar a jiya Jumu’a, tace yan Sanda sun Kama matar ne da misalin karfe 11:40pm na dare bayan sun samu labarin hayaniya a Gidan mamacin.

 

Rundunar Yan Sandan tace ta damke matar ne bayan da Ofishin yanki dake gwadan-gwaji a birnin Kebbi suka jiyo hayaniya cikin gidan mariganyin Mai suna Attahiru Ibrahim dake Aleiro Quarters Kuma gidan a kulle.

 

A yayin da Jami’an Rundunar suka Isa gidan sun iske Ibrahim a kwance cikin jini inda daga bisani likitoci suka tabbatar da ya mutu, inda Kuma faridar da ake zargi take a cikin gidan ta kasa fita.

Talla

Kakakin yace ana zargin matar Kuma tuni aka kama ta domin gudanar da bincike.

 

Yace tuni kwamishinan Yan Sandan jahar Ahmed Magaji Kontagora ya umarci Ofishin yanki na hukumar su tura matar zuwa ga sashen binciken manyan laifuffuka na hukumar dake jihar Kebbi, domin gudanarda cikakken bincike akan yadda lamarin ya faru a cewar Kakakin.

Rahotannin da wakilin Kadaura24 dake jihar Kebbi ya aiko mana na nuni da cewa Farida ta iske tsohon mijin nata ne saboda ta hana shi sake auren da zai yi, Inda ta dade tana bukatar ya Mai da ita dakinta shima yaki.

 

Tuni dai akayi Jana’izar Barr. Attahiru Zagga a masallacin anguwar Aleiro kwatas dake Birnin Kebbi da misalin karfe 10:00 na safen jiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...