Daga Ibrahim Sani Gama
Wata kungiya mai suna dake rajin haɗa kan Kwararrun Masana don goyon bayan takarar Gwamna ta Dr. Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo wato Gawuna/Garo professional political Network. (GAPON) ta sha alwashin hada hannu da kwararru a fannoni daban-daban domin tabbatar da nasarar Gawuna da Garo a babban zabe Mai zuwa a Jihar Kano.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar Ambassador Sadi Garba Sai’d ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai wanda aka gudanar a ofishin kungiyar dake birnin Kano a Juma’ar nan.
Shugaban kungiyar yace kungiyar tana aiki ba dare ba rana don ganin Dr.Nasuru Yusuf Gawuna da Hon. Murtala Sule Garo sun sami nasarar lashe zaben Gwamnan Kano don cigaba da aiyukan da gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya faro wadanda suka sauya fasalin jihar kano baki daya.
Bama So Malam Shekarau da Mutanensa su fice daga NNPP – Abba Gida-gida
” Babu shakka idan Dr. Nasiru Gawuna da Hon. Murtala Garo suka Sami nasara zasu Sanya Kwararru a fannoni daban-daban cikin gwamnatin don su bada ta su wajen gudanar da aiyukan da zasu Kara kawowa jihar kano cigaba ta bannoni da dama”. inji Sadi Garba
” A wannan shi ne karon farko da aka samar da kungiyar irin wannan a duk fadin Arewacin Nigeria wadda ke rajin ganin Kwararrun Masana a fannoni daban-daban sun shiga harkokin Siyasa musamman jam’iyyar APC domin su bada tasu don cigaban jihar kano ” .Inji Amb. Sadi Garba
Shugaban kungiyar ya kara da cewa za su hada kan mutane sama da miliyan daya a birnin Kano da kewaye domin tallafawa tafiyar Nasuru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo wajen ganin an kafa gwamnati ingantacciya da za ta amfanar da al’ummar jihar Kano.
Yadda ambaliyar ruwa ta jawo asarar miliyoyin kudi ga yan kasuwar kantin kwari a kano
” Ya zama wajibi mu samar da wani tsari ko wata taswiyar ko manufa wacce za’a dora jihar kano akan ta, kamar yadda jihar Lagos da sauran jihohin kudancin kasar nan sukai, wanda hakan ne zai samar da cigaba Mai dorewa a jihar kano“
” Zamu hado kan Kwararrun Masana kamar lauyoyi da Injiniyoyi da Kwararrun manoma da likitoci da dai sauransu, domin shiga tafiyar Gawuna da Garo don samar da tsare-tsaren yadda za’a kawowa jihar Kano cigaba mai dorewa“.
Amb. Sadi Garba ya baiwa al’ummar jihar Kano tabbacin cewa in har aka kafa Gwamnatin, al’umma da dama za su amfana saboda dukkanin Gawuna da Garo Mutane ne da suka riƙe mukamai da dama don haka suna da kwarewar da zasu kawo sauyi a rayuwar al’ummar jihar kano.