Yan Bindiga sun Kai hari,Sun yi Garkuwa da Dan Kasuwa a Kano

Date:

Mazauna karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai musu hari tare da garkuwa da wani attajirin ɗan kasuwa a yankin.

Ganau sun tabbatarwa da BBC cewa lamarin ya faru ne da karfe 10;30 na daren Alhamis a garin Kore da ke karamar hukumar, inda suka rinka harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Sun kuma shaida cewa ƴan bindigar da suka kai hari sun kai mutum shida a kan babura uku. Babu dai asarar rai amma an jikkata wani yaro da harsashin bindiga a kunne.

Ƴan garin sun ce lokacin da aka kawo musu harin babu jami’an tsaro da suka kawo musu dauki ko suka zo gurin da al’amarin ya faru.A

Acewarsu mutane da dama sun shiga kaduwa sannan akwai wadanda suka tsere dazuka saboda karar harbe-harben.

Shugaban karamar hukumar Dambatta Muhammad Abdullahi Kore ya tabbatar wa BBC kai harin, sannan ya shaida wanda aka sace a matsayin Emmanuel wanda ke harkokin kasuwancin sa a garin na kore.

Wannan al’amari dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke kokawa da yadda yan bindaga ke taruwa a dajin Falgore a matsayin mafaka, inda ya nemi rundunar sojin Najeriya da su kawo masa dauki wajen ganin yan bindigar basu yi tasiri ba a jihar

225 COMMENTS

  1. Український важковаговик Олександр Усик (18-0-0, 13 ko) зустрінеться в чемпіонському поєдинку за титули wbo, ibo, ibf із британцем Ентоні Джошуа (24-1-0, 22 КО). Anthony Joshua vs Oleksandr Usyk Ентоні Джошуа – Олександр Усик: прогноз букмекерів на бій

  2. Усик Джошуа – смотреть прогноз букмекеров на чемпионский бой 25.09.2021 – Александр Усик проведет бой против Энтони Джошуа – котировки букмекеров AnthonyJoshua Український боксер Олександр Усик (18-0, 13 ko) розповів про те, що його не турбує різниця в розмірах з британцем Ентоні Джошуа (24-1, 22 КО). “Так все життя було. Хтось був більше, хтось менше. Люди, які про це говорять, не до

  3. Антъни Джошуа взима €17,5 млн. за бой с Усик. /КРОСС/ Антъни Джошуа ще заработи 17,5 млн. евро за боя с Александър Усик в събота на стадион „Тотнъм” в Лондон, разкриха британският таблоид „Мирър JoshuaUsyk Усик — Джошуа. Букмекери зробили прогноз на бій. Редкач аргументував такий сміливий прогноз тим, що попередні олімпійські чемпіони, яких побив Джошуа, були на заході кар’єри, тоді як Усик

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...