Daga Auwal Alhassan Kademi
Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Rufa’i Alkali, a ranar Larabar da ta gabata ya ce jam’iyyar a shirye take ta hada kai da wata jam’iyyar kafin zaben 2023 mai zuwa.
Malam Alkali, mai baiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa ne ya bayyana hakan a Legas a wani taron manema labarai.
A cewarsa, jam’iyyar ba ta kyamar tattaunawa da wasu jam’iyyun don gina kasar nan.
“ kowacce jam’iyya tana da damar zuwa mu tattuna Amma Jam’iyyun da ke son tattaunawa dole ne mu bayyana ra’ayoyinmu kan makomar kasar nan.
“Dukkan jam’iyyu daidai suke a doka.
“Muna magana ne game da makomar Najeriya,” in ji Mista Alkali, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa.
Premium Times ta rawaito ya kuma yi tir da yadda ake tafiyar da harkokin siyasa a Najeriya, yana mai cewa bai kamata mutane su zo a tattauna da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso ya janye burinsa na karar Shugaban kasa ba.
Tattaunawar kawance tsakanin jam’iyyun NNPP da Labour ta tsawon makonni ta kasa haifar da sakamakon da ya sa ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun biyu – Kwankwaso da Peter Obi .