Rashin karbar shawarwari da gwamnati ba ta yi ne yasa matsalolin Nigeria sukai yawa – Mumuda Z/Kabo

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama
Al’umma da dama na ci gaba da kokawa dangane da yadda hada_hadar kudaden kasashen ketare ke tafi, musamman Dala wadda da ita ce yan kasuwa dake fita zuwa kasashen duniya suke amfani da ita don yin kasuwancinsu, hakan ya janyo babu tsayayyen farashi da za a dauka a matsayin farashinta.
Akan haka Wani dan kasuwa a kano Alhaji Mamuda Zangon Kabo, wanda yake shi ne Shugaban kungiyar matasan yan kasuwa dake harkokin kasuwancin magunguna a Malam Kato dake jihar Kano, ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da sauran masu Ruwa da tsaki a fannin hada_hadar kudaden kasashen ketare, da su samar da wasu hanyoyi Masu sauki ga yan kasuwa domin su rika samun dala cikin sauki don suma su rika sayar was Mutane kayansu da sauki.
Yace Gwamnatin tarayya tana da rawar takawa a fannin kawo sauyi na kudaden kasashen ketare, inda yace yan kasuwa suna mutukar shan wahala saboda rashin samun kudaden kasashen ketare wadanda suka hadar da Dala da Euro da yans na kasar sin, da sauran kudaden kasashen waje da al’ummar Najeriya suke amfani da su domin yin kasuwanci da yawan Neman lafiya da na shakatawa  a duniya.
Mamuda Zangon Kabo, ya kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohin su yi duk maiyiyuwa wajen bullo da hanyoyin da za su kawar da irin wadannan matsaloli na rashin  dai-daituwar kudaden kasashen Duniya.
Daga karshe ya bukaci Gwamnati ta rika karbar shawarwari daga daidaikun al’ummar Najeriya, kasancewar akwai dubban masu ilimin da za su taimakawa mahukunta da hanyoyin da za su Samar da mafita a harkokin kudaden kasashen ketare da kawo bunkasar tattalin arziki a Najeriya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...