Daga Auwal Alhassan Kademi
Gwamnati jihar kano ta yi alkawarin sake samar da jami’o’i guda 2 a Kano domin Kara bada damar inganta Ilimin matasa a jihar nan.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabin yayin bude taron makon matasa wanda Majalisar dinkin duniya ta ware domin duba kan matsalolin matasa da Kuma lalubo hanyoyin da za’a magancesu, taron a gudanar da shi ne rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.
Gwamna Ganduje yace tuni an tura sunayen kwalejin horar da malamai ta sa’adatu Rimi da Kuma kwalejin koyar da aikin noma ta Audu Bako dake Danbatta ga hukumar da take kula da jami’i ta kasa (NUC) domin neman sahalewa.
Yace yayi hakan ne domin Kara baiwa matasa damar su Kara karatu don inganta Rayuwar da Kuma cigaban jihar kano baki daya..
Idan wadannan jami’o’i suka tabbata Kano tana da jami’o’i guda 4 kenan mallakin gwamnatin jiha.