Gwamnatin kano da Bankin Duniya Zasu Gina Titunan mai tsahon kilomita 6,300 a yankunan karkara

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar bankin duniya da hukumar raya kasar Faransa sun shirya gina titunan karkara mai tsawon kilomita 6,300 a fadin jihar.

 

Darakta Janar na Hukumar Raya Karkara da samar da hanyoyi don fito da amfanin gona ta Jihar (RAAMP), Hon. Yahaya Adamu Garin Ali ne ya bayyana hakan yayin da yake bude horon kwanaki 5 ga mahalarta taron su 152 kan tattara bayanai da dabarun yadda za’a gudanar da aikin a jihar kano.

 

 

Sanarwa da jami’in yada labaran shirin a jihar kano Adamu Abdullahi ya aikowa kadaura24, yace Hon. Garin Ali, ya nanata kudirin Gwamnati na inganta hanyoyin karkara don shiga da fito da amfanin gona a jihar.

 

Don haka DG ya bukaci mahalarta taron da su dauki wannan aiki a matsayin gudunmawar da zasu baiwa jihar kano wanda ke bukatar jajircewa da sadaukar da kai don tabbatar da kokarin gwamnatin jihar kanona inganta rayuwar al’ummar jihar nan.

 

A bangare guda kuma kodinetan aikin na jiha, Engr. Sunusi Sale Suleiman, ya bayyana horon a matsayin cika sharuddan da bankin duniya ya bukata domin aiwatar da aikin da Kuma amfani da manhajar da aka samar do sanya idanu kan yadda ake sarrafa kayayyakin da ake amfani da su a yankunan karkara na Najeriya (NiRTMS) .

 

Engr. Suleiman ya kara da cewa, makasudin gudanar da wannan horon shi ne a koya wa mahalasta taron yadda zasu yi amafani da manhajar da aka samar domin bibiyar aiyukan da aka gudanar a yankunan karkara a fadin jihar kano baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...