Daga Rukayya Abdullahi Maida
Mataimakin Gwamnan Kano, kuma ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana kan sa a matsayin wanda yafi duk sauran yan takarar gwamnan Kano saboda kwarewar sa a harkar gwamanti da Kuma jagorancin al’umma.
” Jama’ar Kano su ne za suyi shaida saboda sun san wane ɗan takara ne yake da cancantr ya jagorance su, da taimakon su za mu yi nasara a zaɓen “, in ji shi.
Musa Iliyasu Kwankwaso na cigaba da daka wawaso a cikin NNPP ta Kura Madobi da Garun Malam
Dr. Gawuna ya bayyana haka ta cikin Wani shiri da aka gabatar a gidan talabijin na kasa wato NTA, mai suna “political update”, kamar yadda yake a ƙunshe cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran da, Hassan Musa Fagge ya fitar a ranar lahadi .
“Wannan gwamantin ta yi ayyuka raya ƙasa da more rayuwa da dama wajen ciyar da jihar gaba “, a cewar Dr. Gawuna.
Yace mukaman da ya riƙe a gwamnatoci guda 3 a Kano da kumu kasancewarsa mataimakin gwamna a yanzu sun sa ya Sami kwarewa da sanin makamar aiki fice da sauran yan takarar na sauran jam’iyyu a Kano.
Mataimakin Gwamnan ya kuma bayyana ɓarakar da sauran jam’iyyun siyasar ƙasar nan ke fama da shi a matsayin ɗaya daga abinda zai tabbatar musu da nasara, ganin yadda APC take tsintsiya maɗaurin ki ɗaya a yanzu.
Dr. Gawuna, wanda yake riƙe da muƙamin mataimakin Gwamnan Kano, ya taɓa riƙe matsayin shugaban ƙaramar hukuma har sau biyu, da na tsohon Kwamishina gona da albarkatun ƙasa sau uku, yanzu haka yana neman kujerar Gwamnan Kano a zaɓen 2023.