KAROTA ta yi nasarar kama wani matashi mai yin sojan gona da sunanta

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Hukumar dake kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA tayi nasarar cafke wani matashi yana sojan-gona da sunan shi Jami’in hukumar KAROTA ne.

 

A cewar mai taimakawa shugaban hukumar kan harkokin kafafen yada labarai na zamani, Ayuba Jarumi, KAROTA ta cafke matashin ne karfe 12 na daren litinin dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci akan titi yana karbar kudi.

 

Matashin mai suna Lukman Abdullahi mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari bayan kama shi ya bayyanawa Hukumar Karota cewar shi ɗan Maiduguri ne.

Talla
Talla

Inda ya kara da cewa yana amfani da kayan ne saboda jama’a su fahimci shi ma’aikacin hukumar karota ne.

 

Dama chan Hukumar ta jima tana samun Rahoton yadda matashin yake amfani da sunanta wajen Musgunawa al’ummar Jihar kano, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.

Rayuwa ta tana cikin Hadari -Hadiza Gabon

Daga karshe shugaban Hukumar ta KAROTA Hon. Dr. Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su cigaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma.

 

Ya kumace da zarar Hukumar tkammala binke akansa zasu miƙa shi hannun jami’an Yansanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar tuhuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...