An saki karin fasinjoji biyar na jirgin kasan Abuja-Kaduna

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

‘Yan bindigar da suka sace fasinjoji a jirgin kasar da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a Najeriya a watan Maris din da ya gabata sun saki karin fasinjoji biyar.

 

Hukumomin tsaro da gwamnatin kasar ba su tabbatar da sakin karin mutanen ba, amma gidan talbijin na Channels TV ya ambato mutumin da ke shiga tsakani domin sako fasinjojin Tukur Mamu yana cewa an saki mutanen ne a yau Talata.

 

Ya bayyana cewa mutanen da aka saka su ne: Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal, Abubakar Ahmed Rufai, Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.

Talla

 

BBC Hausa ta rawaito babu bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin a saki fasinjojin.

Gwamnatin Kogi ta rufe gidajen karuwai, ta kuma hana sanya takunkumi

A watan jiya ne aka saki karin wasu fasinjojin jirgin kasan na Abuja-Kaduna kwanaki kadan bayan ‘yan bindigar sun fitar da wani bidiyo wanda ya nuna su suna lakada musu duka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...