Daga Sani Magaji Garko
Kungiyar tallafawa marayu da masu karamin karfi wato CSADI ta ce ta gano mutane sama da 60 masu dauke da cuta Mai karya garkuwar jiki daga watan Fabarairun 2021 zuwa yanzu.
Shugabar kungiyar Hajiya Zainab Ahmad Suleiman ce ta bayyana hakan lokacin da Kungiyar ta ziyarci hukumar Hisbah ta jihar Kano domin yin aiki hadin gwiwa tsakanin hukumar da Kugiyar.
Hajiya Zainab Ahmad Suleiman ta ce sunce hukumar ne domin hada hanu da nufin yaki da yaduwar cutar HIV da gano cutar da kuma Dora masu cutar akan magani gami da basu shawarwarin yadda zasu kula da kansu.
Shugabar ta ce tun shekaru 15 da suka gabata sukayi aiki da hukumar Hisbah kuma sun sami nasarori masu tarin yawa amma wasu dalilai yasa suka dakatar da aikin.
Hajiya Zainab Ahmad Suleiman ta ce kididdiga ta nuna cewa jihar Kano ta na samun karuwar yaduwar cutar ta HIV a don haka suke cigaba da wayar da kan al’umma da gudanar da gwaje-gwaje gami da gangamin wayar da kan al’umma domin yaki da yaduwar cutar.
Shugabar ta kuma ce kungiyar da Shirin samar da tsarin da zasu rika koyawa mata da matasa sana’o’i musamman Wanda hisbah take kamawa matukar aka gudanar da bincike aka ga kuma suna da ra’ayin kama sana’o’i tare da barin bariki.
A jawabinsa matemakin kwamandan hukumar Mai kula da harkokin yau da kullum Malam Shehu Tasi’u Ishaq ya ce daya daga cikin ayyukan hukumar ta hisbah shine yaki da badala wacce wani bangare ne da ke kawo yaduwar cutar ta HIV.
Ya ce hukumar za ta fito da dabarun yaki da tutunanin aikata badalar wanda hakan zai taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar cutar inda kuma an sami yaduwar ta a koya musu hanyoyin da zasu kula da kansu.
Matemakin kwamandan hukumar ya kuma bukaci al’umma musamman wandanda suke son yi Aure dasu tabbatar an gwada su Kuma matukar aka Sami wani da cutar to suyi tawakkali tare da hakura da juna domin samun masalaha da alumma ta gari.