Rashin tsaro: Rarara ya shirya addu’o’in nemawa Nigeria Zaman lafiya a Kano

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Shahararren mawakin siyasar nan na Hausa, Dauda Adamu Kahutu, wanda a ka fi sani da Rarara, ya shirya addu’a ta musamman a kan rashin tsaro da ke addabar Arewaci da ma wasu sassa na Nijeriya.

An shirya addu’ar ne a Jihar Kano a yau Litinin, da zimmar Allah Ya kawo ƙarshen rashin tsaro a ƙasar.

Da ya ke jawabi a yayin taron addu’ar, Rarara ya ce ya zama wajibi a haɗu a yi wa ƙasa addu’a a bisa mawuyacin halin da ta tsinci kanta.

Talla

A cewar sa, rashin tsaron da ya addabi Arewa da ma wasu sassa a ƙasar nan, na matukar bukatar addu’a, musamman ma yadda babban zaɓe na 2023 ke tunkaro wa.

 

Ya ƙara da cewa Musulmai da Kiristoci ya kamata su duƙufa da addu’a a masallatai da coci-coci domin neman ɗauki daga Ubangiji.

Rarara wanda shi ne shugaban kungiyar 13×13 ya kuma ce taron bashi da wata alaƙa da siyasa, “illa dai a nemo mafita a wajen Ubangiji domin samun zaman lafiya.

“Idan babu zaman lafiya, ko mu ma ba za mu iya yin harkar fim ɗin mu ba. Saboda haka muna kira ga ƴan Nijeriya, Musulmai da Kiristoci, da mu dage da addu’a a masallatai, coci-coci da kuma gida-gida domin Allah Ya bamu zaman lafiya,”in ji Rarara.

Wani Sashin na malaman da sukai addu’o’in

Ya kuma ƙara da cewa taron ya yi amfani wajen kara danƙon zumunci tsakanin ƴan masana’antar Kannywood.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an yi saukar Alkur’ani da kuma yanka raƙumai guda biyu, inda a ka yi sadakar naman domin Allah Ya karɓi addu’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...