Daga Rahama Umar Kwaru
Babban Daraktan Ƙungiyar APC Media and Mobilization Group for Ahmed Bola Tinubu (ABT) na shiyyar Arewa maso Yamma Amb. Aminu Nuruddeen Amin ya miƙa takardun kama aiki ga Hon. Tijjani Sani Amasko da Hon. Kabiru Aluta Dambatta a matsayin director da Secretary na jihar Kano a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comrade Kingsley Omadoye.
Amb. Aminu yace bai yi wannan zaɓi da ka ba sai da yayi zuzzurfan bincike sannan ya gano cewa babu wasu jajirtattun matasa a jihar Kano waɗanda suka shahara wajen tallata jam’iyyar APC da ƴan takarkarinta na kowanne mataki kamar Tijjani Sani Amasko da abokan aikin sa.
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin biyan diyya ga wani gani matashi da aka sara a hannu
Ya tabbatar da cewa idan suka karɓi abu to sunayi da gaske, kuma suna da tsayayyen tsarin da duk saƙon da suka karɓo zasu aikashi kuma zai dire har ƙasa kasancewar suna da tsarin da ya taho daga jiha, shiyya zuwa ƙananan hukumomi ya tafi har mazaɓu.
Amb. Aminu Nuruddeen a madadin shugabanninta na ƙasa ya tabbatar da cewa wannan ƙungiya tana biyayya sau da ƙafa ga jigo a tafiyar Tinubu wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, kuma tuni yana cikin iyayen wannan ƙungiya na Arewa Maso Yamma.
A ƙarshe, An bayar da shawarwari tare da addu’ar Allah S.W.T ya bawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin sa Sen. Kashim Shettima nasara a zaɓen 2023 mai zuwa, Ameen.