Daga Rukayya Abdullahi Maida
Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano tace ta sami nasarar kama yan daba 84 da muggan makamai a yayin bukukuwan Sallah Babba.
Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan yan sanda na jihar Kano CP Samaila Shu’aibu Dikko me ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jami’a na Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.
Sanarwar ta ce an kama yan daba ne a dukkanin Masarautu gudanar biyar da ake da su a Kano, Inda yace an kama su ne a ranakun Hawan Daushe da Hawan Nasarawa da Hawan Dorayi da sauran haye-hayen Sallah da aka yi a sauran Masarautu.
A Cikin sanarwar kwamishinan ya yabawa al’ummar jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro a jihar Kano, bisa gudunmawar da suka bayar har aka samu gagarumar Nasara a yayin bukukuwan Sallar Babba.