Daga Auwal Alhassan Kademi
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta neman izinin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ficewa daga jam’iyyar APC, Saboda hada musulmi da musulmi a takarar shugaban kasa.
Osinbajo ya ce wata takarda da akai ta yada ta, da ke nuna cewa ya nemi Buhari ya ba shi damar ficewa daga APC ba daga gare shi take ba.
Takardar mai kwanan watan Yuni 24, 2022 mai lamba SH/VP/605/2./0 mai take ‘Neman Izinin ficewa daga APC,’ ya lissafa matsalolin da wasu dalilan da suka sa ya yanke hukuncin a cikin takarar.
Da yake mayar da martani, Osinbajo, ta bakin mai magana da yawun sa, Laolu Akande, ya bayyana takardar a matsayin ta bogi.
Akande ya ce Osinbajo ba zai taba yi irin wannan rubutu ba mai cike da kurakurai.
“A ina ku ka samo wannan takarda ? Wa ya baku? don guje wa shakku, waccen takardar ta da da alaka ko ta kusa ko ta nesa ga mataimakin shugaban kasa , “ya gaya wa manema labarai.
Idan zaku iya tunawa, Osinbajo ya zo na uku a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja.
Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso
Kafin zaben fidda gwani na shugaban kasa, an zargi mataimakin shugaban kasar da cin amanar Bola Tinubu, saboda ya shiga neman kujera daya da shi.
Tun a baya Bola Tinubu ubangidan siyasar Osinbajo ne, don haka ya nema masa mataimakin shugaban kasa tun a shekarar 2023.
Yanzu haka, Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a takarar shugaban kasa da yake yiwa jam’iyyar APC.