Daga Hauwa Umar
Wata kungiya mai suna Media and Mobilisation Group BAT mai goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ta nada Aminu Nuruddeen Amin a matsayin darakta na shiyyar Arewa maso Yamma na kungiyar.
Nadin na kunshe ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan Yuli mai dauke da sa hannun Comrade Kingsley Omadoye, Darakta Janar na kungiyar, wadda aka rabawa manema labarai ranar Alhamis a Kano.
2023: Kwankwaso ya zabi Fasto Idahosa a matsayin mataimakinsa
A cewar wasikar, Amin Nuraddeen, dan jarida ne dake gabatar da shirye-shirye a gidan rediyo da talabijin na Liberty a jihar Kano, shi aka dorawa alhakin kula da daukacin jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai.
Bance masoyana su zabi Tinubu ba, Ina nan akan takara ta – Kwankwaso
Wasikar ta kara da cewa an bai wa Malam Amin alhakin damar samar da tsarin shugabancin riko na kungiyar a yankin har zuwa lokacin kaddamar da kungiyar ta kasa a watan Satumba.
“A lokacin ne za a yi biki tare da tabbatar da nadin a hukumance tare da sauran jami’an yanki da na jihohi,” a cewar wani bangare na wasikar.
An haifi Amin Nuraddeen a Kano a shekarar 1985, ya yi digirinsa na farko a fannin harkokin gwamnati a jami’ar Escae-Benin da ke jamhuriyar Benin, yayin da ya samu digirinsa na biyu a fannin hulda da kasa da kasa a wannan jami’a a shekarar 2019.
Malam Amin, yana da aure da ’ya’ya, ya yi aiki a masana’antar yada labarai daban-daban tun daga shekarar 2013.